Top 15 Mushaƙata Da HausaQs Responders

Babban burin shafin HausaTrends® a yanar-gizo bayan haɗa kan al-umar Hausawa waje ɗaya kamar tsintsiya, shine muga mabiyan mu a cikin farinciki da annashuwa. Tabbas haka abin yake domin taken mu ma shine “Kasance Cikin Murmushi Ako Yaushe 😀.

20130910-204028.jpg

Tunanin fara HausaQs yazo mana ne a lokacin da muka fuskanci cewa masu akawunt ɗin Questionnaires suna ɗaya daga cikin masu ciniki sosai a kasuwar tuwitar ƴan Najeriya (Nigerian Twitter Market) . To ashe harkar zata karɓu sosai kuma anan muna miƙa saƙon godiyar mu ga Random Namenj (@Ali_Jubril) wanda (iya sanin mu) shi ya fara irin wannan harkar wato #HausaQuiz ranar 1 ga watan Mayu, 2013. Bayan kwana tara ranar Lahadi 10 ga watan Mayu, 2013, mun cigaba da yin HausaQuiz amma sai muka koma saka hashtag ɗin #HausaQs.
To shine fa abu ya zama jiki duk ran Lahadi da misalin ƙarfe takwas na dare agogon Najeriya sai munyi HausaQs a inda samari da ƴan-mata da yawa ke bada gudunmawar su acikin nishaɗi.

20130910-204458.jpg

20130910-204939.jpg

Hashtag ɗin Mushaƙata yazo ne bayan wata biyu da fara HausaQs (5 ga watan Mayu, 2013) a yayin da muka fuskanci cewa mabiya HausaTrends na son abinda muke yi sosai domin muna ɗebe musu kewa.

20130910-205259.jpg

Mushaƙata Da HausaQs! Yau muna bikin wata shida da fara Mushaƙata Da HausaQs. A saboda hakane mukaga ya dace mu nunawa mafiyawancin masu bin Mushaƙata a mabiyanmu cewa muna karanta amsoshin su sosai ta yadda har mun ɗan gano irin yadda suke tinkarar tambayoyin sannan da kuma wasu sirrika/bayanai dan gane da wannan ƙayataccen shiri.

TOP 15 MUSHAƘATA DA HAUSAQS RESPONDERS

1. Ibrahim Umar Bello (@aaramz)
Tunda Aaramz ya fara yin Mushaƙata Da HausaQs har ran Lahadin da ta wuce bai fasa ba!!! Dalili kuwa shine mu dai ba zamu iya tuna ranar da muka yi shirin bai halatta ba! Shi kaɗai ne mai wannan kwalitin. Saboda hakane HausaTrends ke mai laƙani da “Constant Mushaƙata Da HausaQs Responder“. Yima Aaramz “retweeting da faving” na response ɗinsa ya zama dole. Godiya malala gashin tinkiya dan-uwa. Allah ya ƙara lafiya.

20130910-210320.jpg

20130910-210453.jpg

2. Zaynabou Abou (@zayn89)
Indai a tsarge maka Karin Magana ne daidai-wa-daidai a Mushaƙata Da HausaQs to gaskiya ba kamar Zaynabou. Kuma ta ƙware sosai wajan zaƙulo kalmomin Turanci a cikin kalmar Hausa. Muna godiya ƴar-uwa. Allah ya bar zumunci.

20130910-210739.jpg

20130910-211004.jpg

3. El’Farouq (@mallamson)
Hahaha Mallamson! Babban mabiyin HausaTrends kenan. Mallamson ya ƙware sosai wajan bada “super hilarious” amsar da zata iya ƙulle ma mutum ciki =))! Duk da dai mutane da yawa suna bada amsa mai ban dariya domin harka ce ta ɗebe kewa, amma gaskiya babu wanda ya kama ƙafar Mallamson kuma ya ƙware wajen fidda kalmomin Turanci da Hausa daga kalmar Hausa. Godiya mai yawa ɗan-uwa. Allah ya bar zumunci.

20130910-213438.jpg

20130910-213623.jpg

20130910-213822.jpg

4. SM Ghali (@Ghalight)
Ghalight ‘top lad‘ kenan 😃! Shima yana ƙoƙari sosai wajan tsarge Karin Magana daidai-wa-daida kuma masani ne sosai bangaren sunayen abubuwan gargajiya (babbar harka) sannan kuma akwai ƙoƙari wajan fassara Turanci izuwa harshen Hausa daidai yadda ake buƙata. Muna godiya ɗan-uwa. Allah ya bar zumunci.

20130910-214215.jpg

20130910-220547.jpg

5. Bakatsiniya (@Bakatsiniya)
Katsinawan Dikko kunya gareku ba dai tsoro ba =)). Bakatsiniya akwai ƙoƙari wajan ƙarasa Karin Magana kuma inda take birge mu shine idan bata sani ba zatace ‘ban sani ba’ kai tsaye =)). Kuma akwai ta wajan fassara Turanci zuwa Hausa sosai da kuma fidda kalmomi da yawa a cikin kalma ɗaya. Muna godiya ƴar-uwa. Allah ya bar zumunci.

20130910-220946.jpg

20130910-221128.jpg

20130910-221315.jpg

6. Muhammad (@Mahmood_Moh)
Mahmoud ƙwaro kenan =)). Tsohon mabiyin HausaTrends. Yana ƙoƙari sosai wajan ƙarasa Karin Magana amma gaskiya in dai wajan zaƙulo kalmomi da yawa ne a cikin kalma ɗaya to ba kamar sa. Godiya mai yawa ɗan-uwa. Allah ya bar zumunci.

20130910-225234.jpg

20130910-225704.jpg

7. Aeysha Ibrahim (@siddiqah222)
Siddiqah manyan gari kenan =)). Ɗaya daga cikin manya-manyan mabiya HausaTrends. Itama tana ƙoƙari wajan amsa Karin Magana kuma kamar Bakatsiniya, itama in batasan ƙarashen magana ba takance ‘ban sani ba gaskiya’ =)). Muna godiya ƴar-uwa. Kema Allah ya bar zumunci.

20130910-230052.jpg

20130910-230456.jpg

20130910-230745.jpg

8. Jay BM (@meilahh)
Hahaha Meilah kenan =))! Ita irin Mallamson ne domin a mata babu mai bada ‘funny response‘ sama da ita duk da tana ƙoƙari wajan Karin Magana. Akwai ‘direct translation‘. Godiya mai yawa ƴar-uwa. Allah ya bar zumunci.

20130910-231222.jpg

20130910-231355.jpg

9. Muhammad Saulawa (@Saulawa85)
Muhammad Saulawa shima tsohon mabiyin HausaTrends ne kuma shima da shi aka fara Mushaƙata Da HausaQs. Ƙwaro ‘both sides ‘ kenan musamman wajan fidda kalmomi da yawa a cikin kalma ɗaya. Godiya mai yawa ɗan-uwa da fatan Allah ya bar zumunci.

20130910-231919.jpg

20130910-232556.jpg

10. RIZQ (@PharmAbdull)
PharmAbdul shima tsohon mai bibiyar Mushaƙata Da HausaQs ne. Yana ƙoƙartawa ako wane bangare musamman ma wajan fassara kalamen soyayya da Turanci izuwa Hausa. Muna godiya sosai ɗan-uwa. Allah ya bar zumunci.

20130910-232941.jpg

11. Jarma-03 (@amadumcjago)
Tsohon mabiyin kuma masoyin shafin HausaTrends kenan. Jarma akwai ƙoƙarin taɓa ko ina a Mushaƙata Da HausaQs. Muna godiya ɗan-uwa da fatan Allah ya bar zumunci.

20130910-233239.jpg

20130910-233423.jpg

12. Hafsee (@its_clown)
Hafsee manyan ƴan-mata =)). Duk da bama jinta yanzu sosai ba zamu manta da gudunmawarta ba. Hahaha! Itama akwai ƙoƙari wajan bada amsa mai ban dariya kamar Mallamson da Meilah. Muna godiya ƴar-uwa da fatan kuma Allah ya bar zumunci.

20130910-233839.jpg

13. Abdul AZ (@mii2you)
Abdul ‘the boss‘ =))! Shima tsohon mai bibiyar Mushaƙata Da HausaQs ne kuma akwai ƙoƙari wajan taɓa ko ina musamman Karin Magana. Muna godiya ɗan-uwa kuma da fatan Allah ya bar zumunci.

20130910-234157.jpg

20130910-234333.jpg

14. Fatima (@Fateem_paki)
Fateema Paki ga Hausa ga Turanci =)). Itama akwai ƙoƙari wajan taɓa ko ina a Mushaƙata Da HausaQs musamman ma wajan zaƙulo kalmomi da yawa a cikin kalma ɗaya da kuma Karin Magana.

20130910-234525.jpg

15. Her Royal Highness (@Jormani_)
‘The biggest fan of Mushaƙata Da HausaQs’ kenan 😀. Ita bata ƙi kullun da daddare a dinga yin Mushaƙata ba domin abin yana ɗebe mata kewa sosai. Mu kanmu ta samu farinciki a lokacin da take cewa ai da mahaifiyar ta ma suka shaƙata 😃😀👍. Muna godiya da fatan kuma Allah ya bar zumunci.

20130910-234911.jpg

20130910-235026.jpg

Daga ƙarshe muna godiya ga duk mabiya shafin HausaTrends® na Twitter, Facebook da Instagrammusamman ma masu bibiyar Mushaƙata Da HausaQs. In sha Allah ƙarshen makon nan mai zuwa (Lahadi) zamu canza hashtags din #HausaQs #Mushakata zuwa #MushakataDaHausaQs a haɗe. Sabon canji.
@HausaTrends