Muhimmiyar Shawara Ga Baba Buhari Domin Ceto Kasarmu Nijeriya

Muhimmiyar Shawara Ga Baba Buhari Domin Ceto Kasarmu Nijeriya.
*Ya Kamata Canji Ya Soma Daga Majalisa
* Sanata na karbar Naira Miliyan 36,000,000 kowane wata*. 

Idan aka raba gida biyu yana karbar Naira Miliyan 18,000,000, ragowar *Naira Miliyan 18,000,000 za a iya amfani da su wajen daukar ‘yan Nijeriya 200 aiki kowa ya rika daukar albashin Naira Dubu 90,000 kowane wata.* 

Idan aka yi mutum 200 sau adadin Sanatocin mu 109 hakan na nufin za a dauki ‘yan Nijeriya *dubu 21800 aiki *. 

A takaice ‘yan Nijeriya 200 za su iya rayuwa a wadace da rabin albashin Sanata na kowane wata. 

*Dan Majalisar Wakilai na karbar albashin Naira Miliyan 25,000,000 kowane wata.*

Idan aka raba albashin gida biyu ya zama Naira Miliyan 12.5million a wata. Ragowar *Naira Miliyan 12.5 za ta isa a dauki ‘yan Nijeriya 135 aiki su rika daukar albashin Naira dubu 92,500 a wata*. 

‘Yan Nijeriya 135 sau adadin yawan ‘yan Majalisar Wakilai 360, hakan na nufin za a dauki ‘yan Nijeriya *dubu 48600 aiki*. 

‘Yan Nijeriya 135 za su rasu a wadace da rabin albashin dan Majalisar Wakilai.

 *Don haka Baba Buhari gwamnatin ka za ta iya daukar ‘yan Nijeriya dubu 70,400 aiki da za a rika ba su albashin Naira dubu 90,000 wasu kuma Naira dubu 92,500. Kuma cikin ruwan sanyi ta hanyar RABA ALBASHIN Sanatoci da ‘yan Majalisar Wakilai!!*

Ka gwada yin wannan lissafin ya mai girma Shugaban Kasa….

Yanzu aikin kowane dan Nijeriya ne ya yada wannan sako domin Sanatoci da ‘yan Majalisar Wakilai su san a dalilin albashin da suke dauka mutane nawa ne ba su da aiki a Nijeriya..

Ya kamata SAUYI ya fara daga MAJALISA!

ALLAH YA TAIMAKI NIJERIYA

Daga shafin Sarauniya

Advertisements

1 Comment (+add yours?)

  1. Abubakr_Mashi
    Oct 05, 2016 @ 08:09:24

    Tabbas in da za a tabbatar da wannan kuduri, to lallai za a ceto rayuwar dubban yan Nageriya daga rashin aiki, ya kamata Sanatoci da Yan Majalissu su daina ci da gumin yan Nigeriya.

    Reply

Leave a Reply

Fill in your details below or click an icon to log in:

WordPress.com Logo

You are commenting using your WordPress.com account. Log Out /  Change )

Google+ photo

You are commenting using your Google+ account. Log Out /  Change )

Twitter picture

You are commenting using your Twitter account. Log Out /  Change )

Facebook photo

You are commenting using your Facebook account. Log Out /  Change )

w

Connecting to %s

%d bloggers like this: