Wasu Hadaddun Hotunan Zahra Buhari

20150116-220210.jpg
Ainihin hoton da ya jayo hankalin matasan Najeriya akan Zahra Buhari, yar gidan General Muhammadu Buhari. Da kuma wannan

20150116-220844.jpg
Da wannan…

20150116-220944.jpg
Ita dai Zahra takai kimanin tsawon kwana uku kenan sunan ta ya na jerin Trending Topics a Najeriya ba dan komai ba sai saboda wa yan nan hotunan nata da kuma wata kila wannan…

20150116-221511.jpg
Da wannan wanda ta ke tare da kyakkyawar mahaifiyar ta…

20150116-221708.jpg

Sai dai akwai wasu wa yanda ba su zagaya duniya sosai ba. Wa yan nan kuwa su ne…

20150116-222013.jpg

20150116-222036.jpg

20150116-222059.jpg

20150116-222132.jpg

20150116-222154.jpg

20150116-222218.jpg
Babban abinda ya bawa matasan Najeriya kudu da arewa sha’awa shi ne Zahra Buhari ta samu daukaka nan da nan ta hanyar yaduwar da hotunan ta suka yi ba tare da ta nuna tsiraicin ta ba hatta gashin ta. To da ya kuke tunani? Ai dole a samu yayan General Muhammadu Buhari da tarbiya duk da dai ita rayuwa haka take duk tarbiyar da ka ba dan ka wani zai iya tanbarewa, amma zai wuya ga yayan GMB.

Advertisements

Sai an Kula Kashi ya ke Doyi!

Wa yan da suka kona motar kamfen din GEJ a Jos ba su kyauta ba gaskiya domin hakan zai sa makiya GMB su yada karya da karerayin da suka ga dama. Duk zaben da GMB ya fito bai samu nasara ba babbar matsalar shi rashin hadin kan yan kudu ne. Yanzu abin da yake faruwa a Najeriya ba karya ba ne domin kowa ya gane GEJ ya gaza kuma ba zai iya jan ragamar mulkin kasar nan ba ta yadda hatta manya-manyan fastocin kudu sun yi Allah wadai da shi GEJ din kuma sun ce dole su na bukatar canji saboda haka mutanen su su zabi GMB. GMB yanzu haka ya na kudu ya na gudanar da kamfen din shi lami lafiya kuma ya na samun karbuwa amma sai ga wasu suna neman bata mai damar da ya samu a nan arewa. Kowa fa ya na da hakin tallata kuma zaben wanda ya ga dama kuma ako da yaushe zaman lafiya da kwanciyar hankali muke ta faman nema.
Akwai hanyoyi da dama da zamu hadu mu kada PDP ta yadda ba sai mun tayar da hankalin mu dan kawai wasu tsirarrun munafukai a cikin mu sun fito suna tallata GEJ a wannan lokacin mai wuya. Ku tuna fa bahaushe ya ce sai an kula kashi ya ke doyi. Sai abar banzaye su ta yi tun da an basu kudi suyi ta yi basu da kishin yan uwansu. In sha Allahu GMB sai ya zama shugaban kasa kuma sai ya kawar da babbar matsalar mu na rashin zaman lafiya da kwanciyar hankali a wannan lokacin. In sha Allahu GMB sai ya kawo mana kyakkyawan canjin da al-umma Najeriya zasu amfana.