Mu Kare Daraja da Ƙimar Yaren Mu a Idon Duniya

Wasu yare masu alaƙa da kiristanci suna yaɗa mummunan labari akan Hausawa a intanet wanda ke nuni da ƙiyayya a filin Allah Ta’ala dangane da yaren Hausa da kuma Hausa/Fulani. ‘Yan uwa ya kamata mu farka wajen kare daraja da ƙimar yaren mu a idon duniya ta hanyar ƙaryata labari ko tarihin da suke badawa akan mu ko kuma mu da kanmu, mu bada gudunmawa ta ɓangaren rubuce-rubuce wato ‘blogging’ a intanet.
Domin duk sanda wani ƙabila a duniyar nan zaiyi bincike akan al-adu ko tarihin Hausawa to gaskiya akwai yiwuwar zai iya chin karo da irin ɓataccen jawabi akan mu.
Wannan tunanin ya zo min ne a yayin da nayi wani bincike mai suna “interesting facts on Hausa people” a shafin nan na Google a yayin da nake so nayi amfani da wasu tabbatattun bayanai game da Hausawa a sabon shafin da na buɗe mai suna @HausaFacts_ a Twitter.
Mu ƙabilar Hausa/Fulani Allah ya yi mana ni’ima/baiwa sosai idan mukayi la’akari da addinin musulunci. Kashi 99.90 cikin 100 a Hausawa musulmai ne kuma zai wuya kaga kiristan Bahaushe sai dai idan Bamaguje ne yabi ‘yan ɗarikar katolika (sakamakon sakewar da shuwagabannin mu, sarakunan mu ko masu kuɗin mu suke yi). Kuma munfi kowace ƙabila a Najeriya yawa. Saboda haka, sauran ƙabilun da suke ji da kansu, suna ɓaƙin-ciki da hakan yadda ba’a tunani shiyasa suke kokari wajen ganin cewa sun ɓata mana suna ko sun baƙanta hotunan mu a idon duniya ta hanyar rubuce-rubuce wai harda bada tarihi akan mu. Duk inda akace mutum ba yaren ka bane kuma baida ra’ayin addinin ka, shi zai bada tarihi ko wani bayani akan ka, to ai sai abinda ka gani kawai!
Amma Allah Ya fi su hikima, domin su da kansu suke kama kansu akan abinda suke rubutawa ta yarda komai ƙarancin fahimtar mai karantawa zai gane akwai ƙiyayya a cikin lamarin.
Ya Allah muna roƙon ka da ka ƙare kare mu daga sharrin maƙiya.
Kubi http://www.twitter.com/HausaFacts_ da http://www.twitter.com/HausaTrends1

Advertisements

Jirgin Sama Mai Amfani da Hasken Rana ya Tashi a Karo na Farko

jirgi mai amfani da hasken rana

jirgi mai amfani da hasken rana


Da ga Capt. Auwal Sa’id http://www.twitter.com/auwalsaid2

Ranar Jumma’a a karo na farko a tarihi wasu matuka jirgin sama (pilots) su biyu ‘yan kasar Switzerand, suka tashi daga jihar California ta Amurka a wani yunkurin ratsa kasar da wani jirgi da yake aiki da karfin rana.
Jirgin wanda yake da fukafiki na jirgi samfirin Boeing 747, amma nauyinsa bai wuce na motar-shiga ‘yar tsaka-tsaki ba. Baturan jirgin su suke tattarawa su kuma adana karfin rana, domin jirgin ya sami sukunin tashi dare da rana. Sai dai jirgin baya wuce tafiyar kilomita 69 ko wani sa’a daya, kuma kujerar matuki daya tal jirgin yake da shi,wanda hakan ya tilasta ya rinka tsatstsayawa domin hutu.
Borschberg suna shirin tsayawa a Phoenix, da Dallas, da St.Louis da Washington kamin su sauka a birnin New York cikin watan gobe. Piccard da Borschberg suna kallon balaguronsu cikin wannan jirgi a matsayin mutanen nan na farko da suka fara tuka jiragen sama a duniya. Sun amince lallai ba a kai ga lokacin fara amfani da irin wannan jirgi mai amfani da karfin rana domin kwasar fasinja ba, amma suna fatan hakan zai kai taimaka wajen cigaba da nazarin hanyoyin inganta makamashi da jirage zasu yi amfani da shi.

solar aircraft

solar aircraft


Google Glass: Sabuwar Fasaha

different colours of Google Glasses

different colours of Google Glasses


Abubuwan mamaki basa karewa a duniyar nan. A kullun fannin fasaha ‘kara bun’kasuwa yake yi. Kullun ‘kara kirkiro da na’urorin da ‘karamin hankali ma bazai dauka ba akeyi.
A watan Feburairun wannan shekarar ne kamfanin Google suka fidda wata ‘kayatacciyar na’ura mai kwakwalwa mai suna Google Glass. Shi dai Google Glass wani tabarau (gilashi) ne da ake sawa a fuska wanda yake ‘kunshe da na’urar da ke iya nuna bayanai kamar yadda babbar waya ke yi ba tare da hannun mai amfani da ita ya ta’ba ko’ina ba. Na’ural Google Glass na chu’danya da Yanar Gizo ne ta hanyar umarni da murya.
Ita dai wannan na’ura na aiki ko amfani da Android Operating System ne sannan kuma darajar ma’ajiyar ta takai 16 GB. Tana da camera mai karfin 5 MP wadda take bada damar daukan hoto mai motsi da mara motsi, sannan tana da WiFi (Wireless) da Bluetooth a matsayin hanyoyi biyu da ake jona ta da wasu na’urorin.
Glass na ‘kunshe da Google Applications kamar su Google Now, Google+, Google Maps da Gmail sannan da wasu Applications ‘din da ba na Google ba.
wata mai amfani da Google Glass

wata mai amfani da Google Glass


Wasu daga cikin abubuwan da Glass ke yi ta hanyar bada umarni da murya (wato voice command) sune: daukar hoto mai motsi da mara mosti, yin hira kai tsaye ta Google+, yin bincike akan wani bayani a Yanar Gizo, fassara turanchi i-zuwa wani yaren, nuni zuwa wani waje a duniyar nan, aikawa da sa’ko, bincike akan yanayin gari, bincike akan tafiya ta hanyar jirgin sama da sauran su.
GG Xplorer Ed

GG Xplorer Ed


Shi dai Google Glass ya ‘dan samu ‘kalubale. Dalili kuwa shine bama sai an fa’da cewa duk wani guri da aka haramta amfani da babbar waya ko wata na’urar da ake daukan magana ko hoto mai motsi shim aba za ai amfani da shi ba. A saboda haka akwai gurare da dama inda aka (ko za’a) haramta amfani da shi sannan kamfanin Google din musamman ya hana bada aro ko saidawa ga wani bayan mutum ya siya!
Kudin da aka yanke ma wannan na’urar tabarau shine dalaa dubu-daya-da-dari-biyar ($1,500) kusankwacin naira dubu-dari-biyu-da-arba’in ( N240, 000).
GG hanyoyin sadarwa

GG hanyoyin sadarwa


kubi @HausaTrends1 a Twitter.