Ƙa’idojin Motsa Jiki

Ƙa’idojin Motsa Jiki

Mukan yawaita cewa motsa jiki yana daya daga cikin abubuwan da mutum zai rika yi domin ya samu cikakkiyar lafiya. Hasali ma mukan ce ban da cin abinci mai lafiya, motsa jiki shi ne na biyu a muhimmanci wajen kiyaye cututtuka. 
Don haka muke ba su fifiko. Mun riga mun ga amfanin motsa jiki a wannnan shafi. Da yawa akan aiko tambayoyi a kan hanyoyi da ire-iren motsa jikin da ya dace mutum ya yi. A yau zamu yi bayani a kan ka’idoji da hanyoyi da kuma ire-iren motsa jiki da ya dace da mu.
Hukumar Kiyaye Cututtuka ta Duniya wato CDC da ke kasar Amurka, ta yi makala a kan wannan batu kuma za mu mai da hankali ne a kan abubuwan da ta ce a cikin wannan bayani.
Da farko aka ce ana so kafin mutum ya ce zai fara aikin motsa jiki, ya tabbatar ba shi da wani ciwon zuciya ko na hawan jini ko na sanyin kashi ko na asma. Idan yana da daya daga cikin wadannan, sai likita ya ba shi izini, da kuma nau’in da ya dace da shi. 
Mazan da suka kai shekaru 45 ko matan da suka haura shekaru 55, masana suka ce sai dole likita ya duba lafiyarsu kafin su fara wani nau’i na motsa jiki. 
Dole kuma a kudure cewa fa za a fara ne ba tare da fashi ba, wato ba kiwa, domin idan aka fara aka daina cikin kankanin lokaci to an rasa fa’idar. Wannan kiwa ce takan sa mutane rajista da kulab na motsa jiki ko wata kungiya ta wasanni.
To na’ukan motsa jikin nawa ne? Masanan suka ce akwai nau’i uku: 
Akwai mai kara kwarin jiki wato tsoka da kasusuwa (aerobic) kamar daukar nauyi da ire-irensu, da mai kara lafiyar zuciya da huhu (cardio) kamar gudu ko tafiya mai sassarfa ko tukin keke da ire-irensu, da kuma mai gyara daidaito da yadda gabobi ke motsi kamar ibadar Sallah, da ta yoga da tai chi.
Suka kara da cewa shi nau’i mai wuya, wato irin na aikin daga nauyi, a kan so akalla a yi mintuna 10 a rana ana yi. 
Shi kuma nau’i na biyu mai kara kaifin aikin zuciya, sai an shafe akalla mintuna 15 a rana ana yi kafin a samu fa’idar abin. 
Amma an fi son yin duka biyun ma domin mutum ya samu duka fa’idojin da akan samu. Nau’i na uku kusan kowa yana yi yau da kullum.
A cikin rana guda kuma lokacin da mutum ya kamata ya motsa jiki, ya danganta da son rai.
 Wasu sun fi so su yi da safe, wasu sun fi so su yi da yamma, wasu ma sun fi so su yi da dare.
 Masana suka ce ba wani bambancin lokaci da zai shafi motsa jiki da zai kawo matsala, amma masu yi da sassafe sun fi samun barci mai dadi idan dare ya yi, kuma masu yi da yamma sun fi samun kuzari da karfin ci gaba da motsa jikin.
Ana so kuma kafin mutum ya fara motsa jiki mai karfi ya dan sanarwa jikinsa cewa za a fara aiki. Idan gudu zai yi ya fara da sassarfa, idan nauyi zai daga ya fara da naushin iska misali, kafin a tsunduma ciki sosai. 
Ana kuma so idan an zo karshe a dan sassauta karfin motsa jikin, a sanar da jiki cewa an kusa gamawa. 
Duk wannan yana da alfanu ga lafiyar zuciya da ta tsoka, tunda wasu da sun fara gudu farat daya, nan da nan tsokar cinya kan daure, a samu muscle pull mai ciwo.
Sai shan ruwa. Ana so mutum ya sha akalla lita guda ta ruwa kamar minituna 30 kafin motsa jiki mai karfi, idan lokacin zafi ne ma zai iya sha fiye da haka. 
Ba dai a so mutum ya zo motsa jiki a ji ruwa na gulub-gulub a cikinsa shi ya sa ake sha da wuri. Idan motsa jikin ya wuce minti 30 kamar na ’yan kwallo shi ma sai an kawo ruwa a tsakankani ko ma irin lemon nan mai kara kuzari, wanda masana suka ce yana da amfani idan mutum zai motsa jiki na fiye da awa guda a lokaci daya.
To ya mutum zai gane yana samun fa’idojin? A nau’i na farko mai dan wahalar, mai yi zai ji bugun zuciya ya karu ko ma ya nunka. 
Wato idan mutum zuciyarsa na bugawa sau 80 a minti guda za ta iya kaiwa 160 idan yana motsa jiki mai karfi, idan sau 70 take bugawa a cikin minti guda, za ta iya kaiwa 140 ko ma 150 idan yana motsa jikin. Idan yana so ya yi furuci kuma kalmomi biyu ko uku ne kawai ke iya fita daga bakinsa yayin motsa jiki. 
Da yawa kuma za su ji zufa na karyo musu.
Ke nan idan mutum na motsa jiki amma bugun zuciyarsa bai karu ba, ko numfashinsa bai karfi ba, ba ya samun alfanun da ya kamata. 
Namiji mai sana’ar tsaye, kamar aski ko gugar kaya ko mace mai tafiya a hankali za ta wata anguwa ko wadda ke tsaye a shagon sai da kayayyaki na tsawon lokaci duk ba motsa jiki suke ba a bayanin masanan. 
Sai mutum ya yi wani abu da ya daga bugun zuciya, ya kuma kara karfin numfashinsa na tsawon akalla mintuna goma ake cewa ya amfanu da motsa jiki.
Kada kuma mutum ya zabi motsa jiki wanda zai sa ya rage teba a wani bangare na jiki kamar a mara. Mutane da dama sukan ce su sun fi so kawai su rage teba a mara, abin da wasu ke cewa tumbi, amma ba sa so su rage kibar jiki. 
A bayanin masana ba wani motsa jiki da zai sa irin wannan ba tare da duk jiki ya mori alfanun ba. Misali, motsa jiki na lilon kwance na daga kafafu ko kai wanda wasu suke ganin yana rage tumbi, ba tumbin kawai yake ragewa ba, yakan kara karfin damtsen cinyoyi da na gadon baya.
Ba kuma dole sai jiki ya ji zafi ba ne akan ce an motsa shi, da farko-farko masu motsa jiki sosai za su iya jin dan ciwon cinyoyi ko agara ko damtsen hannu, amma bayan ’yan kwanaki idan wurin ya sabe bai kamata a sake jin wani ciwo ba. Jin gajiya bayan motsa jiki ba matsala ba ce, tunda hakan ma ake so. 
Amma duk wani sabon ciwo mai radadi da hana sakat da aka ji kamar a cinyoyi ko a kirji, a bar motsa jiki a huta, idan bai tafi ba a je a ga likita.

Advertisements

Leave a Reply

Fill in your details below or click an icon to log in:

WordPress.com Logo

You are commenting using your WordPress.com account. Log Out /  Change )

Google+ photo

You are commenting using your Google+ account. Log Out /  Change )

Twitter picture

You are commenting using your Twitter account. Log Out /  Change )

Facebook photo

You are commenting using your Facebook account. Log Out /  Change )

w

Connecting to %s

%d bloggers like this: