FITATTUN TAURARUN KANNYWOOD 10 A TWITTER DA INSTAGRAM 2015

A ƙarshen shekarar 2014, mun yi ƙoƙari sosai wajen zaƙulo fitattun jaruman masana’antar finafinan Hausa wato Kannywood. A wannan shekarar ma dai ba mu gaza ba domin mun tsaya mun yi kyakkyawan bincike wajen gano muku fitattun taurarun a kafafen sada zumunci na Twitter da Instagram.A shekarar 2015 ma dai abubuwa da dama sun faru a kafafen sada zumuncin na Intanet kama daga tashe-tashen hankali da ƙungiyar boko haram ke kawowa, zaɓen shugaban ƙasa da aka yi da samun nasara da Shugaba Muhammadu Buhari ya yi har i zuwa ɓangaren nishaɗi da ɗeɓe kewa musamman ma a masana’antar Kannywood ɗin inda kamar kullum manya-manyan jarumai kamar su Ali Nuhu, Hadiza Gabon, Adam A Zango, Nafisa Abdullahi da sauran su suka taka rawar gani.

Ga yadda lissafin ya canza a masana’antar ta Kannywood musamman ma duniyar Instagram.

A Twitter 

10. Yakubu Mohammed

Yakubu Mohammed shi ya zo na 10 a wannan shekarar in da ya ke da mabiya kimanin 19.1k. A shekarar 2015 dai shi ne ya zo na 9 amma duk da ya samu ƙarin mabiya 10k bai kai ga tsayawa a na taran ba ko kuma ƙasa da haka. 

Yakubu Mohammed

 

9. Bello Muhammad Bello

General BMB ya zo na 9 a wannan shekarar inda ya ke da mabiya 22k. Ya motsa dan a shekarar 2014 shi ne na 10 a inda ya ke da mabiya 9.8k. Hakan ya nuna ya samu ƙarin mabiya 12.2k a cikin shekara ɗaya. 

General BMB da sabon irin wankan da ya shigo da shi

 

8. Fati Washa 

A wannan shekarar ma dai Fati Washa ta riƙe kambun ta na 8 a jerin taurarun da suka fi kowa yawan mabiya a Twitter in da ta ke da mabiya 25.2k. Fati ta samu ƙarin masoya har 13.4k a cikin shekara 1.

7. Mal. Aminu Saira
Mal. Aminu Saira ya na ƙoƙari sosai a ko ina. Duk da wannan shekarar ya sakko daga na 6 ya koma na 7 a inda ya ke da mabiya 28.1k. Babban Darakta dai ya samu ƙarin mabiya 10.8k a wannan shekarar.

Babban Darektan Kannywood kenan

 
6. Sani Musa Danja

Sani Danja ma dai ya sakko daga na 4 a shekarar 2014 zuwa na 6 a wannan shekarar duk da cewar ya samu ƙarin mabiya 9.6k. Danja ya na da mabiya 32.4k a Twitter.  

Wannan shekarar an dama da shi a Nollywood sosai

5. Hadiza Aliyu Gabon

Hadiza Gabon ta yi tashin gwauron zabo in da daga na 7 a shekarar 2014 zuwa na 5 a wannan shekarar da mabiya 33.3k. Gabon dai ta samu ƙarin mabiya har 17k a wannan shekarar. Gaskiya tauraruwar ta na haskawa a ko ina ba ma sai Intanet ba.

4. Nafisat Abdullah

Nafisa dai wannan karon ta yi ƙasa a Twitter in da ta zo na 4 da mabiya 37k ba kamar waccen shekarar ba da ta zo na 3. Ƴar gayun Kannywood dai ta samu ƙarin mabiya har 14k a shekarar 2015.

3. Rahama Sadau

Itama Rahama Sadau ta yi tashin gwauron zabo in da daga na 5 a waccen shekarar ta 2014 zuwa ta 3 a wannan shekarar ta 2015. Rahama ta samu ƙarin mabiya har 21.9k.

2. Maryam Booth

Maryam Booth tananan a matsayin ta na 2 a jerin taurarun da suka fi yawan mabiya a Twitter. Booth dai ta samu ƙarin mabiya har 13.7k. 

1. Ali Nuhu

Ali Nuhu ma dai wannan shekarar shi ya fi kowa yawan mabiya a Twitter Kannywood in da ya ke da mabiya 83k. Sarki Ali ya samu ƙarin mabiya 24.5k. Wannan ya nuna shi ya fi kowa samun mabiya a shekarar 2015 kuma shi ne jarumi na farko a Kannywood da aka fara tantancewa a Twitter.
A Instagram 

10. Saddiq Sani Saddiq

Wannan karon ma SSS ya na nan a na goman shi in da ya ke da mabiya 55.3k. SSS ya samu ƙarin mabiya 48.8k a shekarar 2015.  

SSS a Jos kwanannan

 

9. Aisha Tsamiya

Aisha Tsamiya ta sakko daga na 8 zuwa na 9 a wannan shekarar inda take da mabiya 57.8k. Aisha ta samu ƙarin mabiya har 50.1k a shekarar 2015.  

Aisha Tsamiya

  
8. Halima Atete

Atete ta samu damar haurowa jerin taurarun da suka fi kowa yawan mabiya a masana’antar Kannywood a duniyar Instagram inda ta ke da mabiya har 68.9k kuma ta bama Aisha Tsamiya ratar 11.2k! Atete ta riƙe wuta tana bin ƴan-uwanta bomfa-to-bomfa gaskiya.  

Halima Atete

 7. Adam A Zango

Adam Zango ya sakko daga matsayinsa na 6 zuwa na 7 a wannan shekarar inda yake da mabiya 79.9k. Prince Zango ya samu ƙarin mabiya 70.4k a cikin shekara ɗaya.  

Adam A Zango

 
6. Fati Washa

Fati Washa tana ɗaya daga cikin fitattun taurarun Kannywood 10 a Twitter da Instagram. Washa ta nada mabiya 91.1k kuma ta samu ƙarin mabiya 83.1k. Washeshiyar Yarinya (*dariya)  

Fati Washa

 
5. Nafisa Abdullahi

Nafisa Abdullahi tananan a na 5 ɗinta kamar shekarar data gabata inda take da mabiya 96.6k. Ta samu ƙarin mabiya 86.6k a cikin shekara 1.  

Ƴar gayun Kannywood!

 
4. Maryam Booth

Maryam Booth ta sakko sosai daga Sarauniyar Instagram wato na ɗaya a 2014 zuwa na huɗu a wannan shekarar inda take da mabiya 111k. Maryam Booth ta samu ƙarin mabiya 84.9k.  

Maryam Booth

 
3. Ali Nuhu

Ali Nuhu yana nan a na ukun shi ma a wannan shekarar inda yake da mabiya 116k. Ya sami ƙarin mabiya 94.6k. Ba mu yi bincike ba a Facebook amma dai yanzu haka Ali Nuhu ya na da mutanen da ke bibbiye da al-amuran shi a Facebook din kusan 705.45k wanda hakan ke nuna cewa ya samu ƙarin masoya 341k a wannan shekarar. Harshashe ya nuna a shekarar 2016 Ali Nuhu zai samu masoya miliyan ɗaya.  

Sarki shi ne Kannywood!!!

 
2. Rahama Sadau

Rahama Sadau ta ƙara tashin gwauron zabo a Instagram ma inda ta zo na 2 daga na 4 a waccen shekarar inda yanzu haka take da mabiya 130k. Rahama ta samu ƙarin mabiya 110.4k a wannan shekarar!  

Rahma Sadau ranar birthday ɗinta

 
1. Hadiza Aliyu Gabon

Hadiza Gabon ita ce Sarauniyar Instagram ɗin Kannywood a wannan shekarar inda take da mabiya 134k. Gabon dai ta samu ƙarin mabiya har 111.9 wanda hakan ya nuna tafi kowa samun mabiya a wannan shekarar.  

Tauraruwar Gabon na haskawa sosai

 Mun gode ƙwarai da gaske. Ku bi shafin mu na Twitter, InstagramFacebook da kuma Tumblr 

Advertisements

4 Comments (+add yours?)

 1. Abdallah Bin Yahya
  Dec 30, 2015 @ 23:15:07

  Thanks Hausa Trends!

  Reply

 2. Faisal Kano
  Dec 31, 2015 @ 00:40:11

  Wannan aiki ya yi kyau sosai. Kafin kuma mu kai ga tsara kyaututtuka (Awards) ga gwarazan jaruman namu.

  Amma fa ma su raya al’adunmu, ba ma su raya badala ba. 🙂

  Reply

 3. Ahmad balarabe
  Apr 10, 2016 @ 22:19:56

  Allah yasa mucika da Imani Ameeeeen

  Reply

 4. Bashir
  Dec 10, 2016 @ 20:12:23

  Ilove sarki ali nuhu

  Reply

Leave a Reply

Fill in your details below or click an icon to log in:

WordPress.com Logo

You are commenting using your WordPress.com account. Log Out /  Change )

Google+ photo

You are commenting using your Google+ account. Log Out /  Change )

Twitter picture

You are commenting using your Twitter account. Log Out /  Change )

Facebook photo

You are commenting using your Facebook account. Log Out /  Change )

w

Connecting to %s

%d bloggers like this: