#RanarHausa ta Samu Karɓuwa 

Daga Suleiman Garba Sule (Emlanis)

Ranar Hausa, 26 ga watan Agusta, rana ce ta musamman da aka ware dan ɗaukakin ilahirin Hausawan dake kafafen sada zumunta na yanar gizo musamman Twitter, su nuna ma duniya daraja, ƙarfi da ƙimar yaren su ta hanyar turo da duk tweet ɗinsu tare da tambarin abin batu na #RanarHausa.

An samu nasara sosai domin ko Hausawa da dama sun nuna kishi da alfahari da yaren nasu ta inda suka (suke a halin yanzu haka) tattauna muhimman abubuwa da dama kama daga karin magana, marubuta da littattafan Hausa, mawaƙa da masu wasan kwaikwayo na da da na yanzu, masarautun Hausa, al-adu da dai sauransu. A taƙaice dai #RanarHausa ya shiga jerin manya-manyan abubuwan da aka fi tattaunawa a Najeria wanda shi ne babban burin mu dan ta haka ne abin zai bazu ta ko ina.

   
    
    
    
    
    
    
    
    
    
    
   

Wanda ya fara tunanin ƙirƙiro da Ranar Hausa shi ne Abdulbaqi Aliyu wanda aka fi sani da @Bahaushee inda nan take fitattun akawunt na Hausawa kamar su @dawisu, @Mutan_arewa, @HausaTrends, @HausaPictures da @Hausa24com suka goya mai baya.

   
 Iya sani na da nake da shi na nazarce-nazarce a Twitter, banda shafin @bbchausa da na babban jarumin Kannywood wato @alinuhu, Bahaushe ya fi kowa yawan mabiya a Twitter Hausa inda yake da mabiya sama da dubu sittin da biyu (62.7k) yanzu haka, kuma ya fara amfani da kafar sada zumuncin ne tun watan Mayu shekara ta 2012.

Manya-manyan ƴan jaridu da masu faɗa aji kamar su Aminu Gamawa, Mansur Liman, Omojuwa, Bashir Ahmad, Aliyu Tanko, BBCHausa da dai sauran su, sun tofa albarkacin bakin su a wannan biki mai ɗinbin tarihi da aka fara yau.

Kubi shafukan mu na Twitter @HausaTrends, @HausaPictures, @HausaLovebirds, @HausaFacts_, da @ZaurenLabarai. Zakuma ku iya bin mu a Instagram, Facebook da kuma Tumblr. Mun gode 

Advertisements

Leave a Reply

Fill in your details below or click an icon to log in:

WordPress.com Logo

You are commenting using your WordPress.com account. Log Out /  Change )

Google+ photo

You are commenting using your Google+ account. Log Out /  Change )

Twitter picture

You are commenting using your Twitter account. Log Out /  Change )

Facebook photo

You are commenting using your Facebook account. Log Out /  Change )

w

Connecting to %s

%d bloggers like this: