Sai an Kula Kashi ya ke Doyi!

Wa yan da suka kona motar kamfen din GEJ a Jos ba su kyauta ba gaskiya domin hakan zai sa makiya GMB su yada karya da karerayin da suka ga dama. Duk zaben da GMB ya fito bai samu nasara ba babbar matsalar shi rashin hadin kan yan kudu ne. Yanzu abin da yake faruwa a Najeriya ba karya ba ne domin kowa ya gane GEJ ya gaza kuma ba zai iya jan ragamar mulkin kasar nan ba ta yadda hatta manya-manyan fastocin kudu sun yi Allah wadai da shi GEJ din kuma sun ce dole su na bukatar canji saboda haka mutanen su su zabi GMB. GMB yanzu haka ya na kudu ya na gudanar da kamfen din shi lami lafiya kuma ya na samun karbuwa amma sai ga wasu suna neman bata mai damar da ya samu a nan arewa. Kowa fa ya na da hakin tallata kuma zaben wanda ya ga dama kuma ako da yaushe zaman lafiya da kwanciyar hankali muke ta faman nema.
Akwai hanyoyi da dama da zamu hadu mu kada PDP ta yadda ba sai mun tayar da hankalin mu dan kawai wasu tsirarrun munafukai a cikin mu sun fito suna tallata GEJ a wannan lokacin mai wuya. Ku tuna fa bahaushe ya ce sai an kula kashi ya ke doyi. Sai abar banzaye su ta yi tun da an basu kudi suyi ta yi basu da kishin yan uwansu. In sha Allahu GMB sai ya zama shugaban kasa kuma sai ya kawar da babbar matsalar mu na rashin zaman lafiya da kwanciyar hankali a wannan lokacin. In sha Allahu GMB sai ya kawo mana kyakkyawan canjin da al-umma Najeriya zasu amfana.

Advertisements

Leave a Reply

Fill in your details below or click an icon to log in:

WordPress.com Logo

You are commenting using your WordPress.com account. Log Out /  Change )

Google+ photo

You are commenting using your Google+ account. Log Out /  Change )

Twitter picture

You are commenting using your Twitter account. Log Out /  Change )

Facebook photo

You are commenting using your Facebook account. Log Out /  Change )

w

Connecting to %s

%d bloggers like this: