Fitattun Taurarun Kannywood 10 a Twitter da Instagram

Shekarar 2014 shekara ce da abubuwa da dama suka faru a kafafen sada zumunci na Intanet wanda kusan duk sun taba rayuwar mu ta yau da kullun. Kama daga tashe-tashen hankali da tada kayar banyan da kungiyar Boko Haram ta saka mu a ciki ta hanyar saka mana boma-bomai a duk wani guri da muke gudanar da al-amuran mu na yau da kullun, yin garkuwa da yan-uwan mu, sa yan-uwan mu gudun hijirar dole daga makwancin su da kuma harbe-harbe wanda sukai sanadiyar rasa rayukan ‘yan-uwan mu da dama wasu kuma da dama suka jikkata.Kai harda harkokin siyasa a inda mutane da dama sukai korafi a kan gazawar shugaban kasar Najeriya wato GEJ (Goodluck Ebele Jonathan) dan jam’iyar PDP da kuma yin magana akan GMB (General Muhammadu Buhari), tsohon shugaban kasar Najeriya a zamanin mulkin soja, wanda shi ne dan takarar shugaban kasa a 2015, a karkashin tutar jam’iyar APC, har i zuwa bangaren nishadi, debe kewa da al-adar mu musamman ma a masana’antar Kannywood a inda manya-manyan jarumai kamar su Ali Nuhu, Sani Musa Danja, Hadiza Aliyu Gabon da sauransu suka taka rawar gani.
Wannan ana magana akan Twitter ne kadai kuma duk wani ma’abocin shafin na Twitter ya san a bangaren kasar Hausa irin abubuwan da suka dinga faruwa kenan a wannan shekarar.
Idan aka shiga shafin Instagram kuwa abin ba a cewa komai. Gaskiya Hausawa da yawa sun karu a Instagram a shekarar 2014. Kuma kai kaa ce duk wani dan Najeriya kyakkyawa ne. Tabbas! Idan kana duba Instagram to zaka iya mantawa da duk wani tashin hankali da ke addaban Arewacin Najeriya domin zaka ga kowa na cike da farin-ciki kowa kuma na jin dadin rayuwar shi dai-dai gwargwado musamman ma idan kana biye da shafin Good People (@mutan_arewa) wanda su suka fi kowa yawan mabiya bangaren duniyar Hausawa har taurarin Kannywood. Suna da mabiya sama da 31,000 a halin yanzu. Instagram dai guri ne inda zaka dinga sanar da mabiyan ka (ko masoyan ka) halin da kake ciki ta hanyar tura musu da hoton ka ko hoton wani abu dangane da kai.
Idan kana so ka yi Instagram ana bukatar waya ko wata na’ura wacce ta ke aiki da tsarin iOS ko Android.
To shafin HausaTrends dai ya na ko ina a cikin kafafen sada zumunci biyun nan kuma kasancewar mu ma mun fi karkatuwa ta bangaren al-adar mu, nishadi da debe kewa, daya daga cikin aikin mu ne mun dunga kula da abubuwa da cigaban da ke faruwa a dandalin sada zumunci na duniyar Hausawa.Shi ya sa ake kiran mu da HausaTrends kuma ganin shekarar 2014 ta taho gangara ne ya sa muka ga ya dace mu binciko fitattun taurarun Kannywood guda 10 wa’yanda suka fi kowa mabiya/masoya a shafin Twitter da Instagram.

A Twitter
10. Bello Muhd Bello (@GeneralBMB)
Bello Muhd Bello, wanda aka fi sani da General BMB, ya na da mabiya wajen 9.8k kuma abin sha’awa ga wannan wayayyan jarumi shi ne ya na bin wajen 98% na mabiyan sa. General BMB na kowa da kowa.

9. Yakubu Mohammed (@yakubum71590749)
Yakubu Mohammed, hussainin Sani Musa Danja, wanda aka fi sani a fagen wake-wake amma yanzu harkar fim din ma ba a bar shi a baya ba, ya na da mabiya wajen 10.6k. Har yanzu Mr Yax ya na waka ta Hausa da Turanci.

8. Fati Washa (@washafatii)
Fati Washa, manyan ‘yan mata, tana daya daga cikin fitattun taurarin Kannywood guda 10 wa’yanda suka fi kowa mabiya a duka Twitter da Instagram din. A Twitter ta na da mabiya kimanin 11.3k.

7. Hadiza Aliyu Gabon (@GabonOfficial)
Hadiza Gabon ita ce ta 7 a jerin taurarun Kannywood da suka fi kowa yawan mabiya a Twitter. Fitacciyar yar wasan Hausa mai dinbin yawan masoya a kafafen sada zumunci na Intanet da ma wajen ta baki daya, Gabon ta na da mabiya wajen 16.3k. Saboda sha’awar sauraron masoyan ta a ko ina a fadin duniyar nan, Gabon ta bude babban shafin sada zumunci mai suna dandalina.com inda kowa zai iya bude akawunt domin sada zumunci da ‘yan uwa da abokan arziki.

6. Aminu Saira (@AminuSaira)
Mallam Aminu Saira, mai kamfanin Saira Movies Investment Ltd, wanda kusan a ce mutumin boye ne dan ba a san shi da fitowa a fim ba, sai dai hada fim din kan shi, ya na da mabiya a Twitter wajen 17.3k.A karshe-karshen shekarar nan, Saira ya fito da wani fim mai suna Ali ya ga Ali wanda ya dauki hankalin jama’a da dama saboda kayatarwa da kuma kyau da fim din ya yi.

5. Rahma Sadau (Rahma_Sadau)
Jaruma rahma Sadau ta samu daukaka da farin-jini nan da nan. Rahma, wacce ake kira da (African) Priyanka, tana da mabiya wajen 17.6k a shafin ta na Twitter.

4. Sani Musa Danja (@sanidanja)
Sani Musa Danja, fitaccen jarumi kuma sanannen mawaki a masana’antar Kannnywood, ya na da mabiya wajen 22.8k. Daya daga cikin sabbin wakokin Sani Danja da sukai fice a shekarar 2014 ita ce Alhaji domin ta shiga jerin Trending Topics na Twitter a Najeriya. Sani Danja Alhaji! Alhaji! Alhaji! Alhaji!

3.Nafisah Abdullahi (@nafisatabdulla)
Feenah Baby! Nafisah Abdullahi ta na daya daga cikin manya-manyan taurarin Kannywood masu dimbin masoya a ciki da wajeb Intanet. Feenah ta na da mabiya a Twitter wajen 23k. Tauraruwar dai ta fito a finafinai da dama a shekarar 2014 sannan kuma babban shafin nan mai kawo mana labarai da abubuwan da ke wakana a masana’antar Kannywood wato @Kannywoodscene ya sanar da mu cewa Nafisah Abdullahi za ta fito da sabbin wakokin ta kwanannan.

2. Maryam Booth (@MaryamBooth)
Jaruma Maryam Booth ta na daya daga cikin taurarun Kannywood da suka dade a Twitter. Duk da dai kusan yanzu kamar ta fi bada mahimmanci a bangaren karatun ta da kuma (kamar) kasuwanci, Maryam Booth ta fi ko wace jaruma ko tauraruwa yawan mabiya a duka Twitter da Instagram a inda ta ke da mabiyan Twitter wajen 38.5k kuma ta ba mai bin ta ratar wajen mabiya 15.5k. Jaruma Maryam ba ta cika turo da amon tweet ba yanzu amma da alamun ta fi karkatuwa ga Instagram.

1. Ali Nuhu (@alinuhu)
Babban jarumi Ali Nuhu wanda ake kira da Sarki Ali ya na daya daga cikin fitattun taurarun Kannywood da suka fara yin amfani da Twitter. Sarki Ali yanzu haka ya na da mabiya kimanin 58.5k wanda hakan ya nu na shi ya fi kowa mabiya a masana’antar Kannywood a inda ya bawa mai bin sa ratar wajen mabiya 20k. Jarumtaka, baiwa da kwarewar wannan jarumi ya sa ba a kannywood kadai ya tsaya ba, a a, har masana’antar Nollywood ma ya leka an toya kuma ana tiya waina da shi.

A Instagram
10. Saddiq Sani Saddiq (@SaddiqSaniSaddiq)
Jarumi Saddiq Sani Saddiq, wanda akan kira SSS, ya na da mabiya 6.5k a Instagram kuma shi ne na 10 a jerin wa’yanda suka fi kowa yawan mabiya a Instagram din. A shafin sa na Twitter ya na da mabiya kimanin 7.1k.

9. Aminu Saira (@AminuSaira)
Mallam Aminu Saira ya na da mabiya 6.6k a Instagram a inda ya zo na 9. In aka duba baya za a ga cewa shi ne na 6 a Twitter a wa’yanda suka fi kowa yawan mabiya a Kannywood. Shi dai Mallam Aminu Saira ya kara kuma ya sha gaban fitattun jarumaida dama a Kannywood in aka yi la’akari da mabiyan sa.

8. Aeesha Aleeyu Tsameeya (@Tsameeya)
Jaruma Aeesha Aleeyu Tsameeya ta na da mabiya wajen 7.7k a Instagram.

7. Fati Washa (@washafati)
Fati Washa ma ta na kan gaba a Instagram a inda ta zo na 7 a yawan mabiya da 9.5k. Kamar yadda aka gani a baya, Fati ita ce ta 8 a Twitter a inda ta ke da mabiya 11.3k.

6. Adam A Zango (@de_prince_zango)
Adam A Zango wanda aka fi sani da Prince Zango ya na da mabiya 9.5k. A Twitter kuwa jarumin ya na da mabiya wajen 7.3k.

5. Nafisah Abdullahi (@Nafeesat_Official)
Jaruma Nafisah Abdullahi (Aunty Yalash) ita ce ta 5 a jerin taurarun Kannywood masu yawan mabiya a inda ta ke da mabiya wajen 10k. A Twitter dai Feenah ita ce ta 3 a inda ta ke da mabiya wajen 23k.

4. Rahma Sadau (@Rahma_Sadau)
Rahma Sadau a Instagram ma ba a batta a baya ba domin mabiyan ta na Instagram sun fi na Twitter yawa a inda ta zo na 4 kuma ta ke da mabiya wajen 19.6k a yanzu haka.

3. Ali Nuhu (@RealAliNuhu)
Sarki Ali dai shi ne na 3 a jerin wa’yanda suka fi kowa yawan mabiyan Instagram a Kannywood a halin yanzu a inda ya ke da mabiya kimanin 21.4k. A kwanakin baya ya na saman Hadiza Gabon sannan ya yi yunkurin kamo sananniya Maryam Booth. Amma sai dai kuma tauraruwar Gabon ta haska a inda ta kere shi sannan ita kuma Maryam Booth ta sami gagarumin mabiya musamman a lokacin da aka ba ta mukamin jakadiyar cigaban matan Najeriya. Sai dai mun san
Sarki Sarki ne. Tabbas Sarki Sarki ne dan ba mu yi bincike a kafar sada zumunci na Facebook ba, amma dai jarumin ya na da gayon bayan masoya sama da 364k.

2.Hadiza Aliyu Gabon (@adizatou)
Hadiza Gabon ta zo na 2 a jerin masu yawan mabiya a Instagram a inda ta ke da mabiya wajen 22.1k. A baya dai Gabon ita ce ta 7 a jarumai masu yawan mabiya a Twitter.

1. Maryam Booth (@OfficialMaryamBooth)
Maryam Booth ita ta fi kowa yawan mabiya a jaruman Kannywood a Instagram a inda ta ke da mabiya wajen 26.1k kuma ta ba mai bi mata wajen ratar mabiya 4k. Ba mu san mai zai faru ba a shekara mai zuwa in Allah Ya kai mu, amma a halin yanzu dai Maryam Booth ita ce Sarauniyar Matan Hausawan Instagram din HausaTrends.

To kun ji fitattun taurarun Kannywood guda 10 da suka yi fice a Twitter da Instagram. Daya daga cikin manyan burukan mu a sabuwar shekarar 2015 mai zuwa in Allah Ya kai mu shi ne manya-manyan jarumai kamar su Ali Nuhu, Sani Danja da sauransu, su yi kokari wajen ganin cewa an tantance akawunt din su na Twitter da Instagram domin hakan zai kara karfin aminci ga mabiyan su.

Da fatan Allah Ya kawo karshen Boko Haram, Ya kawo mana canji mafi alkhairi wan da zai zo da cigaba, zaman lafiya da kwanciyar hankali. Rayuwar mu ta dawo dai-dai domin an dade da sace mana sama da kaso 90% na farin-ciki da kwanciyar hankali.
Ku biyo mu a shafin mu na Twitter, Instagram, Facebook da kuma Tumblr. Mun gode sai kuma mun hadu a sabuwar shekarar 2015. In sha Allah.

Advertisements

Leave a Reply

Fill in your details below or click an icon to log in:

WordPress.com Logo

You are commenting using your WordPress.com account. Log Out /  Change )

Google+ photo

You are commenting using your Google+ account. Log Out /  Change )

Twitter picture

You are commenting using your Twitter account. Log Out /  Change )

Facebook photo

You are commenting using your Facebook account. Log Out /  Change )

w

Connecting to %s

%d bloggers like this: