Mai Yasa Ake Ta Magana Akan Abba! #AbbaIsForming

Abin mamaki da ruɗani baya ƙarewa a duniyar nan. Arewacin Najeriya na fama da ruɗanin Boko Haram ta yarda kusan kullun abinda mutane ke tattaunawa a Twitter kenan amma wasu mutanen suna can suna ta sheƙe ayar su.
Wato a haƙiƙanin gaskiya tunda aka kafa Twitter duniyar hausawa bata taɓa samun eclipse of the moon ba sama da na tsakar daren jiya.
Na faɗi haka ne saboda a daren jiyan a lokaci daya naga mutane sama da hamsin suna saka wani saurayi mai suna Abba a gaba a Timeline ɗin HausaTrends.
Hakan yasa (a matsayina na mai kula da shafin a daren), banyi wata-wata ban a kokarta wajen sanin wai mai ke faruwa ne da abban nan kuma wane gwaninta yayi mutane keta kiran sunan sa haka a wannan daren.
Bincike yasa na gane ashe wata zuƙeƙiyar yarinya ce mai suna RoukayyaB http://www.twitter.com/Mss_Ree ta haɗu da wani gagarumin kuskure a rayuwarta. E ye to gagarumin kuskure mana tunda da alamun amon tweets ɗin da ta tura ma mabiyanta bawai tana sane bane: tweets ne masu nuna alamun tana hira da wata babbar aminiyar ta sai aka samu matsala ta tura ma mabiyanta sama da 1200 a maimakon aminiyar ta ta. Babban tweet ɗin shine:

Hoton tweet ɗin da account ɗin RouqayyahB yayi

Hoton tweet ɗin da account ɗin RouqayyahB yayi


Ga kuma wani hoton tweets ɗin na RouqayyahB:
wani hoton tweets ɗin @Mss_Ree da wayar BlackBerry

wani hoton tweets ɗin @Mss_Ree da wayar BlackBerry


To shine fa samari da ‘yan mata suka farmata da Abba, Abba, Abba, Abba, Abba, Abba, Abba, Abba,… ta yarda kafin kace mai har sunan na Abba ya shiga jerin Trending Topics a Kano, Kaduna da Abuja.
Hankalin wasu mata dayawa ya tashi ta yarda har suke nuni da cewa sudai yau suna son ganin Abba in baka haka ba bazasu iya barci ba. Wasu samarin kuma har tutuya suke da sune Abba!
Abinda yaci ma samari da ‘yan matan hausawa a Twitter tuwo a kwarya shine wai shin waye abban nan da @Mss_Ree take faɗa kuma hakan yasa samari da dama sun chanza sunan su zuwa Abba (ko sun haɗa sunan su da Abba).
Shahararren ɗan Kannywood ɗin nan mai farin-jini a idon al-umma musamman ma a zamanin nan na Twitter inda yake sauraran mabiyansa wato Baballe Hayatu (http://twitter.com/bhayatu), shima da alamun an cika mai Timeline ɗinsa da maganar Abba ta inda shima yake chema HausaTrends (yayin da HausaTrends ke cewa:To Allah Ya kyauta.Gaskiya tweet din hatsarine kawai! Ita yarinyar bazaa ce bata iya amfani da twitter kuma ba zaa ce ‘leaked dm’ ba . Abba).
@bhayatu: ..gaskia kam!amma shi din ma da alamar an sanshi kam!wanda dai basu sanshi ba..nasu san shi ba.lol
@bhayatu: ..wannan shi ake kira jalli-joga..ta shafawa kanta salalan tsiya..ta fasawa kanta jakar tsaba,kuma kaji sun bita!!Abba!abba!
Baballe Hayatu ya cigaba da ba HausaTrends wani labari kamar haka:
..wannan saiya tunan labarin wata mata da taiwa wani karya bayan yabar nigeria.tunaninta bazai dawo ba.akace abar maganar…

..akace idan ya dawo za’a tada maganar a kure mai karya.kwanci tashi rannan saiya dawo.aka shiga ana murna,ana oyoyo..
..ai saita fada daki.tace gashi nayi gulma.yau wane ya dawo..ni hajjaju zanci kaza-kazan ubana..

Tuni sunan Abba ya zagaya Najeriya, ma’ana ya shiga jerin sunayen Trending Topics a gaba ɗaya ƙasar kuma har yanzu zancen da nake mutane basu daina magana akan Abba da Mss_Ree ba a Twitter.
Ita dai Mss Ree tuni ta goge amon tweets ɗin daga jerin tweets ɗinta. Kuma anan ba wai ina goyon bayan Mss Ree bane, a’a, akwai tunanin dana yi wanda shiya sa ko duba tweets ɗinmu kuka yi akan wannan al-amari zaku ga da alamun bamu yarda da itace ta turo da wannan tweets ba nayi bincike akan tweets ɗin ta naga gaskiya bata tweeting da yaren Hausa ko kaɗan kuma katsam sai ta turo da wannan tweets da Hausa a wannan yanayi? Sannan ku duba yadda aka fara aiko da tweets ɗin:
@Mss_Ree: Hmmm ke i didn’t even tell you.. he’s so not good if you know what i mean.
bayan wajen minti 20 sai aka ƙara aiko da wannan:
@Mss_Ree: Hmm kawata ban fada miki ba that guy is impotent … Abba yafi iyawa mehn.
To wannan yasa nayi tunanin gaskiya ba ‘leaked DM’ bane kamar yadda mutane ke tunani domin ya za ai tace ‘Hmmm ke i didn’t even tell you.. he’s so not good if you know what i mean’ so wacce nake tunanin tayi mata wannan abu dan ta bata mata taga wannan bomb ɗin bazai sa mutane su harzaƙa sosai yadda take so ba, kawai sai ta sake tashin wani bomb ɗin (wanda inda yarinyar ne ta asali zaata cigaba da bata labari ne daga inda ta tsaya). Bomb ɗin kuwa shine:
@Mss_Ree: Hmm kawata ban fada miki ba that guy is impotent … Abba yafi iyawa mehn.
Kun gani ko? Hmmm i didn’t even tell you… Hmm kawata ban fada miki ba…!!! Wace wawiya ce zatayi irin wannan kuskuren har sau biyu kuma har wajen minti 20 a tsakanin bomaboman? Ai ba irin yarinyar nan bace zatayi irin wannan kuskuren har sau biyu. Saboda haka ina kyautata zaton ba ‘leaked DM’ bane kamar yadda mutane suke zargi kuma kunga Mss Ree tasan Twitter sosai to banji zata iya jin wannan kuskure har sau biyu.
To mai ya faru kenan??? Ta iya yiwuwa babbar aminiyar Mss Ree ce ta turo da amon tweets ɗin da account ɗin ita Mss Reein saboda ta ci mutuncinta a idon duniya (wannan kuma tsakanin sune domin ba’a san me ya haɗa su ba)
Irin abin da ya faru da Maryam Hiyana kenan aka daina jin ɗuriyar ta a doron ƙasa kamar ta mutu.
Ita dai Mss Ree ta goge amon tweets ɗin kuma tunda abin ya faru bata ce komai ba sai kamar awanni uku da suka wuce take cema wata ƙawarta Fateema kamar haka:
@Mss_Ree:
Broadcasting in BBC or CNN wil be far much Educated than on twitter, i never tot u culd stoop soo Low !! 🙀 @Fateema_YS.
Me ye alaƙar Mss Ree da Fateema? Shin itace aminiyar ta ta da muke tunanin tayi mata wannan ta’asa? Mss Ree ta cigaba da cewa:

@Mss_Ree: Dont fool urslf my dear,ur much worse than a bitch,u r a slut saint which show why saints r dangerrous nd undesirable.
@Mss_Ree: He who takes offence when offence is intended is a greater fool.
@Mss_Ree: I think the most insulting thing u can do to som1is to challenge whn he or she is satisfied wit ur Interpretations.
@Mss_Ree: Are you really that Dumb i jst stil cant believe it 😳🙀😳🙀.
@Mss_Ree: I’d like to say thank you to all the bitches who talk behind my back nd make me the center of their lives🎉🎊💃.

Wannan shine hoton Mss Ree kafin wannan lamari ya faru takai ga chanza wani a halin yanzu. Idan kece da gaskiya Allah ya saka miki!

Kyakkyawar Mss Ree da iPhone dinta

Kyakkyawar Mss Ree da iPhone dinta


To Allah ya kyauta. Shawarar da nake bama ‘yan-uwa samari da ‘yan mata anan shine karku sake ku yarda wani ko wata su san password ɗin ku ko su waye domin duniyar nan ba’a yarda da mutane… Na kusa da kai shine mai iya yi maka illah!
Ku bi http://twitter.com/hausatrends1

Advertisements

1 Comment (+add yours?)

  1. deejahkay
    Jun 04, 2013 @ 19:20:29

    Allah ubangiji ya shirya

    Reply

Leave a Reply

Fill in your details below or click an icon to log in:

WordPress.com Logo

You are commenting using your WordPress.com account. Log Out /  Change )

Google+ photo

You are commenting using your Google+ account. Log Out /  Change )

Twitter picture

You are commenting using your Twitter account. Log Out /  Change )

Facebook photo

You are commenting using your Facebook account. Log Out /  Change )

w

Connecting to %s

%d bloggers like this: