Mu Kare Daraja da Ƙimar Yaren Mu a Idon Duniya

Wasu yare masu alaƙa da kiristanci suna yaɗa mummunan labari akan Hausawa a intanet wanda ke nuni da ƙiyayya a filin Allah Ta’ala dangane da yaren Hausa da kuma Hausa/Fulani. ‘Yan uwa ya kamata mu farka wajen kare daraja da ƙimar yaren mu a idon duniya ta hanyar ƙaryata labari ko tarihin da suke badawa akan mu ko kuma mu da kanmu, mu bada gudunmawa ta ɓangaren rubuce-rubuce wato ‘blogging’ a intanet.
Domin duk sanda wani ƙabila a duniyar nan zaiyi bincike akan al-adu ko tarihin Hausawa to gaskiya akwai yiwuwar zai iya chin karo da irin ɓataccen jawabi akan mu.
Wannan tunanin ya zo min ne a yayin da nayi wani bincike mai suna “interesting facts on Hausa people” a shafin nan na Google a yayin da nake so nayi amfani da wasu tabbatattun bayanai game da Hausawa a sabon shafin da na buɗe mai suna @HausaFacts_ a Twitter.
Mu ƙabilar Hausa/Fulani Allah ya yi mana ni’ima/baiwa sosai idan mukayi la’akari da addinin musulunci. Kashi 99.90 cikin 100 a Hausawa musulmai ne kuma zai wuya kaga kiristan Bahaushe sai dai idan Bamaguje ne yabi ‘yan ɗarikar katolika (sakamakon sakewar da shuwagabannin mu, sarakunan mu ko masu kuɗin mu suke yi). Kuma munfi kowace ƙabila a Najeriya yawa. Saboda haka, sauran ƙabilun da suke ji da kansu, suna ɓaƙin-ciki da hakan yadda ba’a tunani shiyasa suke kokari wajen ganin cewa sun ɓata mana suna ko sun baƙanta hotunan mu a idon duniya ta hanyar rubuce-rubuce wai harda bada tarihi akan mu. Duk inda akace mutum ba yaren ka bane kuma baida ra’ayin addinin ka, shi zai bada tarihi ko wani bayani akan ka, to ai sai abinda ka gani kawai!
Amma Allah Ya fi su hikima, domin su da kansu suke kama kansu akan abinda suke rubutawa ta yarda komai ƙarancin fahimtar mai karantawa zai gane akwai ƙiyayya a cikin lamarin.
Ya Allah muna roƙon ka da ka ƙare kare mu daga sharrin maƙiya.
Kubi http://www.twitter.com/HausaFacts_ da http://www.twitter.com/HausaTrends1

Advertisements

1 Comment (+add yours?)

  1. Abubakar Adamu Mashi
    May 31, 2013 @ 05:00:17

    A Gaskiya Wannan Ba Karamin Kallubale Bane Ga Al’umar Hausa/Fulani Ba, Kuma Wannan Ba Saboda Komai Bane Illah Musuluncin Mu, Idan Akayi La’akari Da Mafiyawancin Hausa/Fulani Cewa Musulmai Ne, Don Haka Idan Aka Fadi Sharri Akan Su To Sharrin Yana Komawa Ne Akan Addinin Mu. Saboda Haka Ya Kamata Mu Farka Daga Dogon Barcin Da Muke.
    Allah Ya Taimake Mu Yakuma Kare Mu Daga Sharrin Makiya.

    Reply

Leave a Reply

Fill in your details below or click an icon to log in:

WordPress.com Logo

You are commenting using your WordPress.com account. Log Out /  Change )

Google+ photo

You are commenting using your Google+ account. Log Out /  Change )

Twitter picture

You are commenting using your Twitter account. Log Out /  Change )

Facebook photo

You are commenting using your Facebook account. Log Out /  Change )

w

Connecting to %s

%d bloggers like this: