BANBANCI tsakanin MANIYYI, MAZIYYI da kuma WADIYYI.

BANBANCI tsakanin MANIYYI,
MAZIYYI da kuma WADIYYI.
=====================
banbancindake tsakaninsu:
1. MANIYYI
Maniyyin namiji: ruwa ne mai
kauri FARI wanda yake fitowa
yayin babbar sha’awa kamar
saduwa, ko wasa da farji,
sannan yana tunkudo juna
lokacinda yake fitowa, kuma
warinsa yana kama da warin
hudar dabino, ko damammen
gari, Idan ya bushe yana
kamshin kwai.
Maniyyi mace: ruwa ne
TSINKAKKE, MAI FATSI-FATSI,
wani lokacin kuma yana zuwa
FARI, wanda yake fitowa
yayin babbar sha’awa kamar
saduwa, ko wasa da farji,
sannan yana tunkudo juna
lokacin da yake fitowa, za ta ji
tsananin sha’awa da dadi
lokacin da ya fito, kuma
warinsa yana kama da warin
hudar dabino ko damammen
gari, Idan ya bushe shi ma
yana kamshi kwai, sannan
sha’awarta zai yanke bayan
fitowarsa.
HUKUNCIN fitar MANIYYI shine:
YANA WAJABTA WANKA.
2. MAZIYYI:
Ruwa ne tsinkakke da yake
fitowa, yayin karamar
sha’awa, kamar tunanin aure
ko kuma tuna wacce kakeso,
ko matarka, ko kallon matar
ko namijin da kike sha’awa,
haka kuma yana fitowa yayin
wasa tsakanin miji da mata,
saidai shi ba ya tafiyarda
sha’awa, kuma wani lokacin
ba ma a sanin ya fito.
Malamai suna cewa: Maziyyi ya fi fitowa
mata, fiye da
maza.
HUKUNCINSA shine A WANKE
FARJI GABA DAYA, DA KUMA
INDA YA SHAFA, KUMA A SAKE
ALWALA.
3. WADIYYI
Wani ruwa ne mai KAURI da
yake fitowa a karshen fitsari,
ko kuma karshen bahaya ga
wanda ya jima bai yi ba, yana
fitowa ga wadanda ba suda
aure, ko wadanda suka yi nisa
da abokin rayuwarsu ta aure,
ina nufin namiji ko mace.

Advertisements

Leave a Reply

Fill in your details below or click an icon to log in:

WordPress.com Logo

You are commenting using your WordPress.com account. Log Out /  Change )

Google+ photo

You are commenting using your Google+ account. Log Out /  Change )

Twitter picture

You are commenting using your Twitter account. Log Out /  Change )

Facebook photo

You are commenting using your Facebook account. Log Out /  Change )

w

Connecting to %s

%d bloggers like this: